Monday, 1 April 2019

Atiku yafi Buhari nesa ba kusa ba>>Obasanjo


Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya jaddada goyon bayan da yake baiwa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019 sannan kuma tsohon mataimakinshi, Atiku Abubakar, inda yace yasan Atiku yasan Buhari dan haka Atiku yafi Buhari nesa ba kusa ba.

Obasanjon yayi wannan maganane a lokacin da wasu masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDP suka kaimai ziyara a gidan gonarshi dake Abekuta.

Ya kara da cewa, ba zaka zama abokinshi ba muddin baka son ci gaban Najeriya. kuma dan Adam tara yake be cika goma ba, shima yana da nashi matsalolin amma wannan bai shafin son da yakewa Najeriya ba.

Yace zai ci gaba da gwagwarmayar ganin ci gaban Najerita har zuwa karshen rayuwarshi.

Obasanjo yace Najeriya ba zata ci gaba ba idan muka ci gaba da zama a yanda muke a yanzu ba.

Dan haka ya bukaci 'yan PDP din dasu yi kokarin samun mutanen da zasu kasance da jam'iyyar komai tsanani, su gano munafukan cikinsu su fitar dasu, ta hakane kawai zasu sake kwato mulkin da suka rasa.

Ya kara da cewa a shekarar 2015 yasan da cewa PDP zata rasa mulki domin abin a bayyane yake, amma idan suka tashi tsaye yanzu zasu sake darewa bisa mulkin. 

No comments:

Post a Comment