Saturday, 13 April 2019

Ba gaskiya bane: Idan kunce jama'ar gari muke kashewa to ku kawo shaida: Hukumar sojin sama ta mayarwa da sarakunan Zamfara martani

Hukumar sojin sama, NAF ta musanta ikirarin sarakunan jihar Zamfara na cewa hare-haren da jiragen sojin ke kaiwa na kashe wanda basu ji ba basu gani ba maimakon 'yan bindigar da ake tunanin ana kashewa, NAF tace sarakunan su kawo mata shedar mutanen da aka kashe idan da gaske suke.A cikin sanarwar da ya fitar, me magana da yawun NAF din, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya bayyana cewa ba abune wanda hankali zai dauka ba a ce sojojin na kashe jama'ar gari maimakon 'yan bindigar ba.

Ya kara da cewa, kamin su kai hari sai sun gudanar da bincike na musamman akan gurin da zasu kai harin dan su tabbatar da akwai 'yan bindigar a gurin, kuma sojojin dake kai harin basa jefa bama-bamai inda mata da yara suke da jama'ar da babu ruwansu, idan ma suka lura babu 'yan ta'adda a inda zasu kai hari sukan dawo ne ba tare da kai harin ba.

NAF tace ba zata tsaya wani cece kuce da kowane mutum ko sarakunan ba akan wannan lamari ba dan kada su kawar da hankalinsu akan abinda suka saka a gababa na kawar da 'yan ta'addar.

Yace duk wanda ke da shedar ana kashe wanda basu ji ba basu gani ba ya kawo ta.

No comments:

Post a Comment