Monday, 8 April 2019

Baballe Hayatu, A'isha Tsamiya, Hassan Giggs, Tantiri da sauransu sun yi Allah wadai da wannan hoton na Amina Amal: Zaka rike baki idan kaji amsar data basu

Jarumar fina-finan Hausa, Amina Amal ta yi suna wajan saka hotunan dake jawo cece-kuce a shafukanta na sada zumunta, saidai mafi yawancin lokuta mabiyantane ke Allah wadai da hotunan da take sakawa amma a wannan karon manyan jarumai da dama sun yi Allah wadai da wannan hoton da ta saka.Baballe Hayatu, A'isha Tsamiya, Hassan Giggs, Abdulmumin Iliyasu, Tantiri na daga cikin jaruman da suka yi Allah wadai da wadannan hotunan na Amina. Saidai ta basu amsar cewa ta gode da shawara kuma itama tana fatan Allah ya shiryeta(wa ya tuna abin da me littafin Ahalari yace?)

Daga baya kuma sai ta sake saka irin wannan hoton dai.
No comments:

Post a Comment