Thursday, 4 April 2019

Babu Abinda Buhari Ya Tabuka A Yankin Arewa>>Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa ya caccaki shugaban kasa Muhammadu Buhari. Bafarawa yace Shugaban ya gaza yin abunda ya dace a Arewacin Nijeriya.


Bafarawa wanda ya fadi hakan a wata fira da yayi da sashin Hausa na BBC yace Babu abunda shugaba Buhari ya tabuka a yankin Arewa. Yace yanzu haka ana safarar mutane, kazalika matsalar garkuwa da mutane, babu dama kayi tafiya tsakanin kaduna Abuja, ga kuma harin 'yan ta'adda sai karuwa yake yi.

"Me muka samu a Arewa? ba cigaba a fannin ilimi, Kasuwanci kam ma ba'a maganar sa a Arewa" Bafarawa yace idan babu wanda zai yi magana akan wannan a Arewa,  mutane irin sa dole su fito su fadi gaskiya saboda yana daga cikin wadanda suka bada gudunmawa don ganin shugaba Buhari ya samu mulkin Nijeriya.No comments:

Post a Comment