Saturday, 13 April 2019

Ban cewa Hadiza Gabon 'yar madigo ba>>Ummi Zeezee


Bayan da wasu labarai suka watsu na cewa tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta ce  Hadiza Gabon 'yar Madigo ce sannan ta mata barazanar sawa a koreta daga Najeriya saboda abinda tawa Amina Amal, Ummi ta fito ta karyata wannan labari.

A sakon data fita ta shafinta na Instagram, Ummi tace, bata ce Hadiza Gabon 'yar Madido bace saboda bata taba kamata ido da ido ba, tace Hadizar tana ganin girmanta sosai dan ko sunan ta bata kira dan haka ita kuma duk me ganin girmanta tana girmamashi.

Ummi ta kara da cewa, idan ma zata shiga fadan Hadiza Gabon da Amina Amal to saidai ta musu sulhi dan kuwa ita yayarsu ce a masana'antar.

Tace wasu matsoratane suka shirya labarin saboda sun san cewa ita bata da tsoro takan yi magana akan ko wanene.

Gadai cikakken abonda tace:


No comments:

Post a Comment