Sunday, 28 April 2019

Barcelona ta daga kofin Laliga bayan doke Levante 1-0: Messi ya kafa muhimman tarihi

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta lashe kofin Laliga na 26 bayan data doke kungiyar Levante daci 1-0. Lionel Messi ne ya ciwa Barca kwallon da ta bata nasara inda shi kuma kofin Laliga na 10 kenan da ya dauka a zamanshi a kungiyar.
Messi ne ke da yawan kofin Laliga fiye da kowane dan wasa daya bugawa Barcelona, kamin wannan lokaci Andres Iniesta ne ke kan gaba da yawan kofunan Laliga 9. Dan kwallo daya ne yanzu a gaban Lionel Messi wajan yawan kofunan Laliga, wannan kuwa ba kowabane illa tsohon dan kwallon Real Madrid, Paco Gento wanda keda kofunan Laliga 12 kuma shine dan kwallon da yafi kowane yawan kofin na Laliga. Messi yaci kwallonne bayan da aka sakoshi daga benci inda cikin mintuna 16 da shigowa ya jefa kwallon a raga, wannan yakai jimullar kwallayen da yaci bayan da aka sakoshi fili daga benci zuwa 24 a gasar Laliga, babu dan kwallon da ya kafa irin wannan tarihi a karnin da muke na 21, sannan yana da jimullar kwallaye 34 kenan.

Real Madrid ce ke gaban Barcelona a yawan daukar kofin na Laliga inda take da yawan kofunan har guda 33.

Yanzu dai abinda ke gaban Barca shine wasan kusa dana karshe da zasu buga da Liverpool wadda ba kanwar lasa bace, musamman idan akazo gasar Champions League.

No comments:

Post a Comment