Wednesday, 17 April 2019

Barcelona ta fitar da Man U daga gasar Champions League: Wannan ce rashin nasara mafi muni da Man U ta yi cikin shekaru 53: Messi ya kafa tarihi


Barcelona ta lallasa Manchester United da ci 4-0 jimulla inda ta fitar da ita daga gasar cin kofin zakarun turai. A wasan da suka buga jiya, Barca taci kwallaye 3 ta hannun Messi da yaci 2 da Coutinho da yaci daya wanda haka yasa aka tashi wasan 3-0.Magoya bayan Man U sun rika caccakar Ashley Young, kamar dai a wasan farko inda suka yi fatan a sayar dashi. Hakanan kuskuren golan Man U din,David De Gea ya bayyana a fili inda shima aka rika caccakarshi da dora mai laifin kwallon da Messi yaci.

Rabon da aci Manchester United irin wannan kwallayen shekaru 53 kenan, tun lokacin da aka kawo dokar zuwa gidan kowace kungiya a buga wasa.

Hakanan Messi ya kafa irin tarihin tauraron dan kwallon Tottenham, Heung-Min Son wanda yaci kwallo daga wajen 18 da kafafun dama da hagu a gasar Champions League a shekarar 2014, Messi ma ya kafa irin tarihin a wasan na jiya, bayan shekaru biyar da wanda Son yayi.


No comments:

Post a Comment