Sunday, 7 April 2019

Barcelona ta kara nisa a saman teburi

Barcelona ta bayar da tazarar maki 11 a saman teburi bayan 2-0 da ta ci Athletico Madrid a zazzafan wasan hamayya da suka buga a daren Asabar.


Luis Suarez da Lionel Messi ne suka ci wa Barce kwallaye masu kyan gaske, wanda ya kara dora su a hanyar lashe kofin La Liga na biyar cikin shekaru bakwai.

Tun kafin a tafi hutun rabin lokaci a kori tsohon dan wasan Chelsea Diago Costa bayan ya ci mutuncin alkalin wasa Jesus Gil a minti na 27.

Su kuwa Suarez da Messi ba su bari damar ta kubuce ba.

Suarez ne ya fara jefa kwallo ana saura minti biyar a tashi daga wasan, inda Messi ya ci kwallo ta biyu dakika 60 bayan haka a minti na 86.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment