Monday, 15 April 2019

Bayan sasanta Ali Nuhu da Adam A. Zango, MOPPAN ta dauki matakin ganin hakan be sake faruwa ba

Bayan sasanta Adam A. Zango da Ali Nuhu, kungiyar MOPPAN ta dauki matakin ganin irin abinda ya faru tsakanin jaruman be sake faruwa ba nan gaba.Kannywoodexclusive ta ruwaito cewa:

AN HANA 'YAN FIM CIN MUTUNCIN JUNANSU A YANAR GIZO. Gammayar kungoyin masu shirya Finafinan Hausa, na MOPPAN da kuma AFMAN, sun haramtawa 'yan Kannywood yada jita-jita, da kuma zage-zage, ko kuma musgunawa wani dan fim a social Media. Lamarin ya biyo bayan nasarar sulhunta Ali Nuhu da Adamu Zango da kungiyoyin su ka yi da yammacin jiya Asabar,  Yanzu haka an kafa kwamitin da zai sanyawa 'yan fim ido game da irin wainar da suke toyawa a shafukan su na social Media. Kwamitin ya ce a shirye suke su hukunta tare da ladabtar da duk wani dan fim da aka gani yana cin mutuncin dan uwan sa a yanar gizo.

No comments:

Post a Comment