Saturday, 6 April 2019

Bazan iya kishi da Gwaggo ba: Ku rufamin asiri>>Martanin Sa'adiya Kabala kan labarin dake cewa tana son auren gwamna Ganduje

Bayan da akaita yada jita-jita cewa tauraruwar fina-finan Hausa, Sa'adiya Kabala ta bayyana cewa babu wanda take so ta aura a Duniya kamar gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Sa'adiya ta fito ta mayar da martani akai.A wani sako data fitar ta shafinta na Instagram, Sa'adiya tace, ta ga wasu hotuna da aka hada nata inda ake cewa wai tace babu wanda take so ta aura sai gwamnan Kano, tace ita bata ce haka ba.

Abinda ta sani shine ta taba yin rubutu a baya tace tana son gwamnan Kano a matsayinshi na dan siyasa amma ba da maganar aure ba.

Sa'adiya ta yi kira ga masu watsa labarin da cewa, ita bata san ma wanda ya kirkiri wannan labari ba dan haka karyane kuma su rufa mata asiri ba zata iya kishi da Gwaggo ba, su barta inda Allah ya jiye ta.

No comments:

Post a Comment