Monday, 1 April 2019

Benzema ya kafa tarihin da Ronaldo da Messi basu dashi


Karim Benzema celebrates his winner against Huesca
A wasan da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta buga da, Huesca, shahararren dan wasanta, Karim Benzema ya kafa tarihin da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi basu dashi bayan kwallon da ya ci a wasan.

Benzema ya kafa tarihin saka kwallo a ragar duk wata kungiya daya hadu da ita a tahirin buga wasanshi a gasar Laliga. 

Tun bayan zuwanshi Real Madrid, kusan shekaru 10 kenan da suka gabata,  Benzema ya hadu da kungiyoyi 34 kuma ya saka kwallaye a ragar kowace kungiya.

Ronaldo da Messi ba su kafa irin wannan tarihi ba.

A cikin kungiyoyi 40 da Messi ya hadu dasu, ya zura kwallo a ragar kungiyoyi 37, kungiyoyin da be taba cinsu kwallo ba sune, Cadiz, Murcia, da Huesca. Shi kuwa Ronaldo a cikin kungiyoyi 33 da ya hadu dasu, ya zura kwallaye a ragar kungiyoyi 32, kungiyar da be taba ci kwallo ba itace, Leganes.

Benzema ya goge tarihin da Hugo Sanchez ya kafa, wanda kamin Benzeman shi kadai ne keda tarihin cin kowace kungiya da ya hadu da ita a gasar Laliga, saidai shi ya hadu da kungiyoyi 33 ne yayin da shi kuma Benzema ya hadu da kungiyoyi 34.

Raul ma ya ci kungiyoyi 35 da ya hadu dasu a gasar laliga, saidai akwai guda 4 da bai samu saka kwallo a ragarsu ba.

No comments:

Post a Comment