Sunday, 14 April 2019

Bincike: Musulmai sun fi kowa wadatar zuci


Bincike: Musulmai sun fi kowa wadatar zuci
Wani binciken da jami'ar Mannheim ta Jamus ta gudanar wanda kuma aka wallafa a mujallar American Psychological Association, ya nuna cewa Musulmai sun fi mabiya sauran manyan addinai, wadanda suka hada da Kiristanci da kuma Yahudanci, nutsuwa da wadatar zuci.Shin Ko me yasa ? Ayar tambayar kenan da masana suka dasa ?


Shi mece alakar wadatar zuci,yarda da kaddara da kuma kwanciyar hankalin Musulmai da kuma addininsu,wato Musulunci ? Kadan kenan daga cikin tambayoyin da masana da kuma manazartan yammacin duniya ke ci gaba da yunkurin samun amsoshinsu.

Kazalika an gano cewa, Musulmai na da wadatar zuci sakamakon yadda kansu ke hade,inda kowa ke iya kula dan uwansu a sauwake ba tare da wata matsala,akasin mabiya sauran manyan addinai.

Masanan na Jamus sun tambayi mutane sama mutane dubu 67 masu shekaru mabambanta, wadanda suka fito daga kasashen daban-daban na duniya game da irin rawar addininsu ke takawa a rayuwarsu.

A cewar wani rahoto da suka wallafa, Musulmai sun fi kowa yakinin cewa rayuwarsu na a hannu wani abin bauta mai girman gaske.Sai kuma Kirista wadanda ba su gabatr da kawunansu a matsayin 'yan shiyyar Katolika ko kuma na Protestan,inda mabiya addinan Buddha da na Hindu ke mara musu baya.Zindikai (wato marasa ubangiji) sun fi kowa karancin hadinkai,kazalika babu kowa daya tak da ke kyatato zaton rayuwarsa na a hannun wani abin bautan da ya fi girma da kuma kima.Duk da cewa masana a fannin ilimin lissafi sun gano wani sirri da ke nuna cewa akwai babbar akala tsakanin hadin kai da kuma wadatar zuci.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment