Saturday, 6 April 2019

Bincike: Yawan dadewar da mutane suke a duniya ya karu

Wani rahoto da Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar ya bayyana cewar daga shekarar 2000 zuwa 2016 shekaru matsakaita na rayuwar dan adam sun karu da shekaru 5.5 wanda ya karu daga 66.5 zuwa 72.


Rahoton ya ce, yawan kudaden da mutane ke samu na taka rawa sosai wajen tsayin rayuwarsu inda tsawon rayuwa a kasashe matalauta yake kasa da na kasashe masu kudi da shekaru 18.1.

Rahoton ya kuma yi hasashen cewar a shekarar 2019 za a haifi mutane miliyan 141 da suka hada da maza miliyan 73 da mata miliyan 68 kuma shekarun mazan matsakaita zai kai 69.8 inda na matan kuma ya kama shekaru 74.2.

Kasashen Japan da shekaru 84 da Swizalan da 83 ne kan gaba a yawan dadewa a duniya inda Lesotho da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suke da mafi karanta da shekaru 52 zuwa 53.

Rahoton ya ce, a karon farko an gudanar da bincike kan nau'in halitta game da dade wa a duniya inda aka gano mata sun fi maza dadewa sosai.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment