Monday, 1 April 2019

"Budurwar Ronaldo zata sake haifa mishi jariri"


A wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da kasar Portugal ta buga da Serbia a ranar Litinin wanda shahararren dan wasanta, Cristiano Ronaldo ya samu bugawa kuma har ya samu ciwo, budurwarshi,  Georgina Rodríguez ta je kallon wasan inda aka ga alamar ciki a jikinta.

Kalar kayan da Georgina Rodríguez ta saka a ranar sunsa anga kamar alamar ciki a jikinta wanda zai zama da na biyu da zata haifawa Ronaldo, shi kuma zai zama na biyar a wajanshi.

A baya dai Ronaldo ya bayyana cewa 'ya'ya 7 yake son ya haifa kuma kowannensu sai ya cimai kyautar Ballon d'Or, watau daidai da lamba 7 da yake goyawa kenan.

Saidai 'yan kwanaki bayan wancan rade-radi da aka rika yi, Georgina Rodríguez ta fito ta ce bata da ciki.

A wata hira da ta yi da Hola, tace, yanayin abincin da take cine, ta jera kwanaki 4 tana cin taliya kuma a jirgi take tafiye tafiyenta shiyasa jiinta ya fara mata nauyi.

Ta kara da cewa har yanzu bata gama murmurewa ba daga haihuwarta ta farko ba

No comments:

Post a Comment