Wednesday, 10 April 2019

Champions League: Juventus da Ajax sun tashi 1-1: Ronaldo ya kafa tarihin da babu me irinshi

Juventus da Ajax sun tashi 1-1 a wasan da suka buga a daren yau na Quarter Finals na neman cin kofin zakarun turai, Ronaldo ne ya ciwa Juve kwallo daka ana gaf da za'a tafi hutun rabin lokaci.

Saidai David Neres ya farke kwallon ta Ronaldo inda ya ciwa Ajax kwallo 1. Wannna yasa magoya bayan Ajax din suka dawo da shewar da suke yi a baya, bayan da kwallon da Ronaldo ya ci su tasa suka yi tsit.

Wannan kwallon da Ronaldo yaci itace kwallo ta 125 da yaci a gasar cin kofin zakarun turai, 

Hakan dai yasa Ronaldo kaiwa yawan kwallaye 24 da yaci a Quarter Final na gasar Champions League wadda babu wani dan kwallon da ya taba cin kwallaye masu yawan haka.

Ajax dai ta fi Juventus taba Kwallo a wasan, saidai Juventus ta samu kwallon waje daga.

No comments:

Post a Comment