Wednesday, 10 April 2019

Champions League: Tottenham ta lallasa Manchester City 1-0

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta lallasa abokiyar karawarta, Manchester City da ci 1-0 a wasan da suka buga a daren jiya na Quarter Finals na neman cin kofin Champions League, duk da cewa babban dan wasanta, Harry Kane ya samu rauni mintuna 11 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, hakan baisa jikin 'yan wasan Tottenham din mutuwa ba.An dai yi tsammanin cewa irin abinda ya faru da Liverpool a wasan karshe na cin kofin zakarun turai na karshe da aka buga zai faru da Tottenham din, inda bayan samun raunin babban dan wasanta, Mohamed Salah, jikin 'yan wasan Liverpool fin ya mutu, Madrid ta yi kaca-kaca dasu kokuma irin abinda ya faru da Madrid din inda suma suka sha kashi a hannun Ajax a wasan rukunin 'yan 16 na gasar Champions League din wanda babban dan wasansu, Sergio Ramos be buga ba amma sai gashi bayan fitar Kane 'yan wasan Tottenham sai suka ma kara kaimi wajan kai hare-hare masu tada hankali a gidan Manchester City.

Son Heung-Min ne ya ciwa Tottenham kwallo inda a haka aka tashi wasan 1-0.

Gadukkan alamu shidai Son yana samun karin kuzarine idan Kane baya nan, lura da a farkon shekararnan da Kane ya samu rauni, Son ya jera wasanni hudu a jere yana ciwa Tottenham kwallaye amma Kane na dawowa sai ya shafeshi.

Bayan kammala wasan, me horas da 'yan wasa na Tottenham din, Pochettino ya bayyana takaicinshi akan rashin lafiyar ta Kane inda yace ga dukkan lamu ba zai dawo ba har zuwa karshen kakar wasan bana, inda ya tabbatar da cewa wasanninsu na gaba ba zasu zo musu da sauki ba.

Masu sharhi dai na ganin cewa, Rashin Kane ba zai zama matsala ga Tottenham ba a wasanta na gaba inda zata bi Manchester City gida, ana tsammanin dai wasan tare zasu yi amma idan ma suka yanke shawarar fitowa su nemi kwallo, basu da matsala.

Ta bangaren Manchester City kuwa sun tafka babban rashi bayan da Sergio Aguero ya barara da bugun Fenareti wanda da ya cishi da watakila labari ya canja.

Danny Rose ya rika samun yabo daga wajan magoya bayan Tottenham.

Kwallon hannun da aka duba na'ura ta jawo cece-kuce.

Wani abu da shima ya dauki hankula a wasan na jiya shine yanda wani me goyon bayan kungiyar Tottenham din yayi kutse cikin filin wasan.

Amma dai duk da wannan sakamako ba za'ace Manchester City ta fice daga gasar ba.

No comments:

Post a Comment