Sunday, 28 April 2019

City ta koma ta daya a teburin Premier bayan doke Burnley 1-0

Saura wasanni bibiyu a kammala gasar cin kofin Premier ta bana, bayan da Manchester City ta dare kan teburi da tazarar maki daya.


Da kyar da gumin goshi City ta yi nasara da ci daya mai ban haushi a gidan Burnley a karawar mako na 36 da suka yi ranar Lahadi a Turf Moor.

Serio Aguero ne ya ci kwallon kuma na 20 a Premier shekarar nan, bayan da ya buga tamaula ta haura layin raga, amma Matthew Lowton ya fitar da ita, wadda tuni alkalin wasa ya karbi cin da City ta yi.


Da wannan nasarar da City ta yi ya sa ta haye kan teburin Premier da maki 92 da tazarar maki daya tala da Liverpool wadda take ta biyu.

Tun bayan da Tottenham ta fitar da City a gasar cin kofin Zakarun Turai ne, kungiyar ta ci wasa uku ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba.

Ta fara doke Tottenham a Ettihad, sannan ta ci Manchester United a Old Trafford da kuma yin nasara a gidan Burnley.

City wadda tun farko ta yi damarar lashe kofi hudu a bana, yanzu tana fatan lashe Premier da FA, bayan da tuni ta lashe Caraboa na shekarar nan, bayan da aka fitar da ita a Champions League.

Sauran wasannin Premier da suka rage wa City:

Premier League 06 Mayu 2019

Man City v Leicester
Premier League 12 Mayu 2019

Brighton v Man City
BBChausa.

No comments:

Post a Comment