Sunday, 14 April 2019

Da Allah ya saka Arziki da Mutuwa a hannun mutane da mu 'yan fim mun shiga uku>>Ado Gwanja

Tauraron mawakin mata kuma jarumin fina-finan Hausa, Ado Isa Gwanja ya caccaki masu zagin 'yan fim inda yace hassada ce ke sasu zagin ba wani abuba, Ado ya bayyana hakane a shafinshi na sada zumunta.A wani bidiyo da ya saka, Ado yace da Allah ya saka mutuwa da Arziki da lafiya a hannun mutane da su 'yan fim kam sun shiga uku, yace shi dai gashi a cikin gidanshi wanda nashine kuma da harkar fim ya gina kuma duk masu zaginasu ba wani abune ba hassadace tasa su suke hakan.

No comments:

Post a Comment