Friday, 12 April 2019

Daliba Daga Jigawa Ta Lashe Gasar Lissafi Ta Kasa

ABIN ALFAHRI GA AL'UMMAR JIHAR JJIGAWA

Wata Dalibar Makarantar  GJSS Mallammadori Mai Suna  Khadija Adamu Salisu, A Jihar Jigawa Ta Lashe Gasar Lissafi Ta Kasa Baki Daya Wacce Aka yi A Birnin Tarrayya Abuja. 


Tun Farko Sai Da Dalibar Ta yi Nasara Har Sau Biyu Yayin Da Aka yi Jarabawar A Matakin Jihar Jigawa. 

Wakilin RARIYA Ya yi Kokarin Jin Ta Bakin Shugaban Makarantar Da Dalibar Ta fito Malam Musa Buraima, Sai Dai Dukkanin Wayoyin Basa Shiga, Har Zuwa Lokacin Da Muke Wallafa Wannan Labarin.
Rariya


No comments:

Post a Comment