Sunday, 14 April 2019

Daliba 'Yar Nijeriya Ta Kafa Tarihin Da Aka Yi Shekaru 100 Ba A Kafa Shi Ba A Kasar Indiya

Wata daliba 'yar Nijeriya ta kafa tarihi a kasar Indiya inda ta kafa wani tarihi da aka dade ba a samu ba kusan shekaru 100 inda ta samu kyaututtuka har guda 20.Dalibar, tsohuwar daliba ce a Jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto mai suna Stella Emelife Chinello wace ta gama digirin ta a Jami'ar ta Sokoto a bangaren Chemistry da matakin shaidar karatu na first class. 

Stella dai bayan zuwa Indiya ta karya wani tarihi da aka dade ba a kafa ba har tsawon shekaru 100 inda ta samu kyaututtuka har guda 20 da kuma wasu kyaututtuka kudade.

Stella dai
ta kafa wannan tarihin ne a Jami'ar Mysore dake kasar Indiya.

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri


No comments:

Post a Comment