Saturday, 6 April 2019

Dan majalisa yayi alkawarin bayyana albashin da ake biyanshi da kuma bayar da albashin kyauta

Wani dan majalisar wakilai da aka zaba kwanannan me suna Akin Alabi ya bayyana cewa da zarar an rantsar dashi ya fara karbar albashinshi zai bayyanawa Duniya nawane albashin da 'yan majalisar wakilai ke karba.Ya kuma kara da cewa, zai kuma bayar da albashin nashi kyauta dan a yiwa jama'ar mazabarshi aiki, watakilama ya kara da kudun aljihunshi.

Alabi yace ba dan neman kudi yaje majalisar ba sannan yana ganin rashin sanin albashin 'yan majalisar ne yasa akewa aikin nasu hangen dala.


No comments:

Post a Comment