Friday, 19 April 2019

Dan wasan baya da a gaba dayan kakar wasan bana babu dan kwallon da ya wuce shi

Tauraron dan kwallon Liverpool, Virgil van Dijk dan wasan da a gaba dayan wasannin da ya buga a gasar Premier League da Champions League na bana har yanzu ba'a samu dan kwallon da ya zo gabashi ya wuce da kwallo ba.Shine dan wasan baya a gasar Premier da ya zama tauraron dan kwallon wata wanda ba'a samu irin haka ba tun shekarar 2013.

Da aka tambayeshi ko yaya zai yi wajan tare Messi a karawar da zasu yi a wasan kusa dana karshe na Champions League? Ya bayyana cewa bai san yadda zata kasance ba dan wasan ba tsakaninsu su biyu bane saidai ranar tukuna.

Ana dai kallo Messi a matsayin wanda ya iya yanka kuma ya zama gagara badau a wajan 'yan baya ko yaya karawarshi da Virgil van Dijk zata kasance?

Lokaci be bar komai ba

No comments:

Post a Comment