Tuesday, 2 April 2019

Danganta Buhari da zaben Kano neman dakushe farin jininshine kawai>>Fadar shugaban kasa

A karin farko tun bayan da aka kammala zaben gwamna a Kano wanda ke cike da dambarwa inda kungiyoyi da dama suka yi tsokaci kala-kala akai, sannan wasu suka rika kira da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya saka baki, wasu kuma suka rika ganin laifinshi akan abinda ya faru a Kanon, fadar shugaban ta fito ta yi bayani.A hirar da yayi da BBChausa, me magana da yawun shugaban kasar, Malam Garba Shehu yace, kiraye-kirayen da ake yi akan Buhari ya soke zaben gwamnan Kano ko kuma ya kwace daga hannun wani ya ba wani bashi da wannan hurumi.

Garba yaci gaba da cewa, idan fa aka tuna shima Buharin sau uku yana zuwa kotu daga kasa har sama dan bin kadin zaben da aka murde masa. Duk wanda ke ganin an yi mai ba daidai ba kuma yana da hujja sai yaje kotu.

Ya kara da cewa, wannan abinda wasu ke yi na danganta Buhari da zaben na Kano kawai an so a dakushe farin jinin da yake dashi a idon talakawane, saboda an yi duk abinda za'ayi amma ba'a yi nasara ba shine aka koma wannan salon, Garba ya kara da cewa, ana tunanin a zabe me zuwa Buharin zai iya cewa mutane su zabi wane su kuma zaba shine ake kokarin dakushe farin jininshi.

No comments:

Post a Comment