Monday, 15 April 2019

Facebook, Instagram da WhatsApp sun daina aiki

Shafukan sada zumunta na Facebook da Instagram har ma da manhajar sakonni ta WhatsApp sun fuskanci matsaloli na tsawon fiye da sa'a uku ranar Lahadi.


Wani shafin intanet mai kula da ko shafukan intanet na aiki ko fuskantar matsala, Down Detector, ya ce mutane a sassan duniya daban-daban sun koka da rashin samun shafukan uku wadanda dukkansu mallakin kamfanin Facebook ne.

Lamarin ya fara ne daga misalin karfe 11:30 agogon Ingila.

Masu amfani da Facebook sun rika samun wani sako da ke cewa "Wani abu ba ya aiki yadda ya kamata" a duk lokacin da suka nemi bude shafin.


Da karfe 2:50 na rana, shafin ya sanar da cewa an warware dukkan matsalolin da suka addabi ayyukansa.

Wani kakakin kamfanin ya fitarda wata gajeriyar sanarwa kamar haka:
"A yi mana afuwa saboda dukkan matsalolin da ku ka fuskanta."
Kamfanin Faceboo bai ce uffan ba dangane da dalilin daina aikin da shafukan suka yi, kuma bai ambaci yawan mutanen da matsalar ta shafa ba.

A watan Maris na bana Facebook ya gamu da babbar matsalar da ta sanya masu ziyartar shafukan Facebook da Instagram har da WhatsApp suka kasa shiga na tsawon fiye da sa'a 24.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment