Wednesday, 10 April 2019

Fadan Ali Nuhu da Adam A. Zango: Adam A. Zango yace ya hakura

Bayan zagin da tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya zargi abokin aikinshi, Ali Nuhu da turo yaranshi suna mai, sannan shi Adamun ya rama akan Alin, lamarin da har ga alama ya tunzura Alin shima yaso ya mayar da martani, a yanzu dai Adamun yace ya hakura.A cikin wasu jerin bidiyo daya wallafa a shafinshi na sada zumunta, Adam yace yana godiya da masoya da abokan arziki da suka bashi bakin cewa fitina bata da amfani, dan haka ya hakura kuma yana kira ga kanne da yaranshi da kada wani ya sake zagin Ali Nuhu ko yaranshi, ko kuma ya mayar da martanin zagin da za'a mai.

Adam A. Zango dai ya bayyana cewa, ya so ya saka hotunan mutanen da ya sama dake kusa da Ali Nuhu wanda ya kai musu korafinshi da dadewa akan lamarin cin mutuncinshi da yaran Alin ke yi wanda kuma ba'a dauki mataki ba.

Yace, Alin yakan bada amsar cewa yaranshi basa jin magana. Saidai shi Adam yace yaranshi na jin maganarshi kuma komai ya wuce, amma nan gaba zai rika saka shafukan da aka bude kacokan dan a rika zaginshi a duk lokacin da suka zageshi dan jama'a su shaida.

Tuni dai Adam ya goge sakunan zagin da ya rama akan Ali Nuhu.

Shi kuwa Ali Nuhu tun ranar da Adam din ya fito da wannan magana, yaso ya mayar da martani amma da dama,masoya da abokan arziki suka bashi baki, daga nan be sake cewa komai ba.

No comments:

Post a Comment