Tuesday, 16 April 2019

Fadar shugaban kasa da wata 'yar fim din kudu da ta yi korafi akan matsalolin Najeriya sun yi musayar yawu

Fadar shugaban kasa da tauraruwar fina-finan Kudu, Omotola Jalade Ekeinde sun yi misayar kalamai bayan data ce jama'ar Najeriya na fama da kansu a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.Omotola Jalade Ekeinde ta yi zargin cewa mutane na gasuwa a mulkin Buhari saboda kudi basu zagayawa sannan ga cin zarafi da kuma kisa da jami'an tsaro kewa mutane, ga rashin tsaro inda ta bukaci gwamnatin da ta yi wani abu.

Bashir Ahmad me taimakawa shugaban kasa akan harkar sabbin kafafen sadarwa ya mayar mata da martani inda yace, masu neman kudi ta hanyar halaliya basu da matsala kuma ba zasu taba kiran kasarmu da sunan da kika kirata dashi ba. Daga shekarar 2015 zuwa 2018 akwai kanana da matsakaitan kamfanonin sarrafa shinkafa da aka bude a Kano,kimanin 200 kuma hakan ya kawo samun kudi tsakanin jama'a.

Omotola Jalade Ekeinde ta kara da cewa, da kake nuna alamar kamar ba ta hanyar data dace nake neman kudi ba, na jika. Tabbas an samu ci gaba ta wani fannin amma kana nufin cewa baka san da matsalar da ake ciki ba? Amma abin tambaya anan shine babu yanda za'ayi mutum yayi magana akan Najeriya sai ace yana goyon bayan wata jam'iyyane?

Bashir ya bata amsar cewa, ta ambaci sunan shugaba Buhari da mataimakinshi Osinbajone wanda yakewa aiki shiyasa ya tankata kuma batun matsaloli tun shekarun 1950 muke tare da wasu tsalolin. Bashir ya kara da cewa mu 'yan Najeriya da muke nuna kamar muna da matsala shin muna biyan haraji?

Omotola Jalade Ekeinde ta kara da cewa, shiyasa wasu basa yin korafi akan harkar gwamnati, a duk lokacin da na yi magana irin wannan zasu fara takuramin da maganar biyan haraji. Tace ammafa idan kasar ta lalace me kudi da talaka kwa sai yaji a jikinshi.

Tace ita 'yar gwagwarmayace kuma ta caccaki gwamnatocin baya fiye da wadannan saidai tana fatan a wannan karin abubuwa zasu canja

No comments:

Post a Comment