Monday, 8 April 2019

Fallasar Asirin Kisan Rayuka Da Ake Yi A Zamfara

Yanzu na gama sauraran video wanda Ash-Sheikh Dr. Abdullah Gadon Kaya yayi takaitaccen bayani akan abinda yake faruwa a Zamfara, yace:


Bari na fada muku wani sirri, zamu fada don ya yadu saboda manya suji, wani zaiyi tambaya wai me yasa aka mayar da hankali akan Zamfara ake ta kashe mutane?

Wato akwai wasu ne daga cikin manyan Kasarnan, lokacin fadar sunansu bai yi ba, amma na sansu, manya ne kuma 'yan arewa ne, suna da ra'ayi akwai arziki ne a jihar Zamfara, ana diban zinare da arzikin dake karkashin kasa da ake tonowa, don haka manyan su suke da hannu wajen diban kayan arzikin suna fitar dasu kasashen waje suna samun dunbin dukiya

Idan aka bar mutane hankalinsu ya kwanta za'a dinga ganin ana fita da dukiya, don haka za'ayi magana, to yanzu sai aka mayar da gurin a tayar da hankalinsu, yanzu mutanen gurin ta rayukansu suke da dabbobinsu da abincin da zasuci su rayu, can kuma inda ake diban arzikin suna can suna diba wallahi, wannan shine abinda yake faruwa a Zamfara

Kuma abin yana da alaka da manya ne shiyasa abin yaki cinyewa, suna da alaka da sojoji, suna da alaka da Gwamnoni suna da alaka da jami'an tsaro, duk wani babba da yake wannan jihar ta Zamfara idan ma zaiyi magana akan kisan da akeyi to akwai wani abu da ake tsakura masa a bashi toshiyar baki, don haka gwanda suyi ta kashe mutane a kasa samun zaman lafita suyi ta diban arziki

Yanzu kamar rikicin da akayi a Borno, Sambisa da sauransu akwai fetur ne a gurin, akwai arziki ne a gurin, idan aka bari hankali ya kwanta ba'ayi ta fadace fadace ba to ai hankali zai koma ace gwamnati taje ta fara diban wannan arzikin don mutane su amfana

Duk abinda kuka ga anayi na zubar da jinin mutane a Kasarnan wallahi akwai hannun musulmai 'yan arewa manyan Kasarnan akwai hannunsu a ciki, kawai munafurci ne ake ba'a fada

Yanzu da zaran mutun ya tara mutane ya fadi gaskiya sai a turo jami'an tsaro su tafi da mutum don basa so a fadi gaskiya, amma a matsayin mu na 'yan Kasa wajibi mu fadi gaskiya ko zasu kashe mu...~Inji Dr. Abdullah Gadan Kaya

Kawai sauran bayanai da yayi a cikin videon, zan tura videon a group WhatsApp na Dattawablog daga na 1 zuwa 10 Insha Allah wadanda suke tare dani a WhatsApp sai suje su saurara

Hakika Dr Abdallah yayi jihadin da ba kowa zai iya ba, yace ya fadi wannan gaskiyar ne ko da za'a kashe shi, banyi tsammanin akwai malamai mujahidai irin shi da suka saura ba tun bayan gushewar su Malam Ja'afar da Malam Albaniy Zaria

Allah Ka tsare mana Dr Abdallah Gadon Kaya daga dukkan sharri da makirci Allah Ka daukaka darajarshi duniya da lahira, Allah Ka nuna mana karshen masu hannu a kisan rayuka da ake a Nigeria Amin.
Datti Assalafiy.


No comments:

Post a Comment