Wednesday, 10 April 2019

Gabon ta shiga sahun batutuwan da aka fi tattaunawa a Najeriya bayan tuhumar data wa Amina Amal akan zargin yi mata kazafin Madigo

Bayan bayyanar bidiyon da aka ga tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon na tuhumar abokiyar aikinta, Amina Amal akan kazafin data zargeta da yi mata na yin Madigo inda a wasu lokutan hadda duka, batun ya shiga sahun batutuwan da aka fi tattau nawa akansu a Najeriya.Baya ga shafukan Facebook da Instagram, batun ya shiga sahun batutuwa hudu da aka fi tattaunawa a shafin Twitter kuma jama'a da dama sun bayyana ra'ayoyinsu akai.

Nafisa Abdullahi wadda itama sannaniyar jarumace na daya daga cikin wanda suka bayyana ra'ayoyinsu akan wannan lamari inda ta rubuta cewa:

Menene wannan, wa ya basu izinin dukanta? Na tabbata ko iyayenta ba zasu mata irin wannan abuba, kawai dan sunga ita karamar yarinyace.

Ta kara da cewa, kawai dan sunga Aminar ba kowa bace shiyasa suka mata haka, amma ita bata goyon bayan cin zarafi irin wannan, sannan kuma harda laifin ita Aminar data zubar da kanta a wajan mace kamarta.

Saidai ra'ayin Teema Makamashi ya banbanta dana Nafisar inda tace, dama Aminar ba 'yar fim bace zuwa ta yi dan ta bata musu suna kuma karya tawa Hadiza Gabon din.


No comments:

Post a Comment