Tuesday, 30 April 2019

Gwamnatin Tarayya ta dauki layoyin kasar Saudiyya dan ganin an sako Zainab Aliyu

Bayan umarnin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya baiwa ministan Sharia akan yayi dukkan me yiyuwa wajan ganin an sako Zainab Aliyu daga kasar Saudiyya da aka kama bisa zargin ta'ammuli da miyagun gwayoyi, hukumar Hajji ta kasa ta dauki lauyoyin kasar Saudiyyar dan ganin sun taimaka wajan sakon Zainab.Hadimin shugaban kasar, Bashir Ahmad ne ya tabbatar da haka ta shafinshi na Twitter.

No comments:

Post a Comment