Wednesday, 10 April 2019

Hadiza Gabon ta turke Amina Amal kan kazafin Madigo data zargeta dashi: Lamarin ya jawo cece-kuce

Wasu bidiyo sun bayyana a shafukan sada zumunta inda aka ga jarumar fina-finan Hausa, Amina Amal sannan ake jin muryar Hadiza Gabon a bayan fage, Amina na baiwa Hadizar hakuri akan kazafin da ta zargi Amina da mata na Madigo.Shafin Kannywoodexclusive ya wallafa hotunan bidiyon guda biyu, na farko anga Amina Amal a tsugunne tana baiwa Hadiza Gabon hakuri sannan Hadizar tana mata tambayoyi akan kazafin data mata inda har take cewa bata san sanda ta rubuta wancan sako ba kuma sharrin shedan da kwayane.

A bidiyo na biyu kuwa anga Aminar a yayinda Hadiza Gabon ke kai mata duka tare da bukatarta ta karanta wani sakon chat da suka yi.

Ra'ayoyin mutane ya banbanta akan wadannan bidiyo, inda wasu ke yabon Hadizar akan abinda tawa Amina, wasu kuwa na ganin hakan be dace ba.  hakanan wasu na ganin akwai dai lauje cikin nadi, lura da wasu kalamai da suka bayyana a bidiyon.

Daya daga cikin masu kwalliya na Kannywood, Mansur Makeup na daya daga cikin wanda suka bayyana rashin jin dadinsu akan abinda ya faru da Amina Amal inda yace koda yake dai ita ta jawa kanta dan bata jin shawara.

Ya kuma bayyana cewa be ji dadin kwace mata shafinta na Instagram da ka yi ba.
Ga dukkan alamu dai yanzu babu shafin na Amina Amal a Instagram saidai ta bude wani sabon shafi.

Muna fatan allah ya kyauta.
Ga bidiyo na daya

Ga bidiyo na biyu

No comments:

Post a Comment