Saturday, 13 April 2019

Harin Sojoji ta sama yasa 'yan bindiga sun dawo cikin gari suna rayuwa da mutane rike da bindigu a Zamfara

A yayin da sojojin Najeriya ke lududen wuta ta sama akan maboyar 'yan bindiga a jihar Zamfara dan ganin  an kawo karshen hare-haren da suke kaiwa jama'ar gari na ba gaira babu dalili, 'yan bindigar sun gujewa maboyarsu inda suka dawo rayuwa da mutane a cikin gari.Wani dan jihar ta Zamfara ya bayyanawa Premiumtimes cewa, 'yan bindigar sun dawo rayuwa da mutane a cikin gari inda ake ganinsu a kauyukan, Jaja, Rukudawa, Tsanu dake karamar hukumar Zurmi, suna yawo da bindigu kiri-kiri kuma babu wanda ke iya musu magana ko kumama iya kallonsu sau biyu.

Ya kara da cewa suna sayen kayan abinci kuma suna da masu kai musu rahotanni akan duk wani abu dake wakana, ya kara da cewa sukan kwana a cikin kauyukan dan gudun harin da sojoji ke kai musu wasu lokutan kuma idan dare yayi sukan koma cikin daji su kwana amma da rana sai su dawo.

Wani shima ya cewa, hari ta sama kawai ba zai yi maganin 'yan bindigar ba sai an saka jami'an tsaro kuma sai gwamnati ta hada hannu da sarakunan gargajiya wajan wannan yaki domin wasu sarakunan na Zamfara nada kyakkyawar alaka da 'yan bindigar.

Ya kara da cewa a shekarar 2016 a lokacin da sarkin Zurmi, Abubakar Atiku zai aurar da diyarshi manyan 'yan bindigar da dama sun halarci bikin inda suka bashi gudummuwar shanu sannan kuma wani sanannen mawakinsu daga kasar Nijar, Sani Danyaya ya zo ya tayasu nishadi su da karuwansu.

Saidai da Premiumtimes ta tuntubi kakakin 'yansandan jihar, Mohammed Shehu ya bayyana mata cewa 'yan bindigar basu da gurin buya kuma lokacine kawai zasu ragargajesu, ya kara da cewa abinda suke bukata shine hadin kai daga wajan jama'ar da abin ya shafa.

No comments:

Post a Comment