Monday, 1 April 2019

Hausawa sun fi kowace kabila gaskiya da tsoron Allah a Najeriya: Karanta yanda 'yan kudu ke ta yabawa Hausawa


'Yan kudancin Najeriya na ta yabawa Hausawa a dandalin Twitter, inda suka bayyanasu da cewa sune kabila mafi gaskiya da kirki a kasarnan. Wata ce ta fara wannan magana inda tace, ta shafe shekaru tana fitowa kofar gidanta da jarkoki masu cin lita 25 guda biyu, ta tsaida Bahaushen dan Acaba ta bashi jarkokin da dubu 8 tace ya sayo mata mai a gidan mai dan ta sakawa janaretanta, idan sun dawo ta biyasu dari 3, tace bata taba samun wanda ya gudammata da kudiba.

Saka wannan labari nata ke da wuya sai jama'a da dama suka nuna jin dadinshi tare da bayar da kalar nasu labaran na yanda suka yi ma'amala da Hausawa kuma mafi yawanci sun nuna gaskiya a ma'amalar da saukin kai.


No comments:

Post a Comment