Saturday, 13 April 2019

Hukumomin tsaro na binciken yunkurin Atiku na hana rantsar da Buhari a karo na biyu


Buhari election
Rahotanni sun bayyana cewa, hukumomin tsaron kasarnan sun dukufa wajan binciken yunkurin da ake zargin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar da yi dan ganin ba'a rantsar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba a watan Mayu.


Wasu rahotannin siriri kamar yanda The Nation ta ruwaito sun bayyana cewa ana binciken wasu mutane da ake tsargi suna da hannu a lamarin kuma ana kallon wannan lamarine a matsayin cin amanar kasa.

A farkon makonnan ne dai aka ga wasu fastocin dan takarar shugaban kasar na PDP a babban birnin tarayya, Abuja inda suke dauke da wasu rubuce-rubuce masu cewa, na ainahi, ingantacce.

Kuma shafin The Cable ya ruwaito cewa Atiku ya biya wani kamfanin kasar Amurka dala dubu 30 dan ganin kamfanin yayi magana da kasar Amurka akan kada ta amince da Buhari a matsayin zababben shugaban kasa saboda hannun da jam'iyyar APC ke dashi wajan murde zaben shugaban kasar da ya gudana.

Atiku dai ya ce karyane wancan zargi da ake masa dan shi be biya kowace kamfani akan a hana rantsar da Buhari ba.

Saidai The Cable tace ta samu takardun da Atiku ya biya kudin kuma kamfaninne da kanshi ya tabbatar mata da haka.


No comments:

Post a Comment