Monday, 15 April 2019

Idan muka yi nasara a wasanni hudu nan gaba to mun dauki firimiya>>Salah

Tauraron dan kwallon Liverpool, Mohamed Salah ya bayyana cewa idan kungiyarsu ta yi nasara a wasanni 4 da zata buga nan gaba to sun lashe gasar Firimiya kenan.Salah ya bayyanawa Sky Sport haka a wata tattaunawa da ta yi dashi inda yace yana bibiyar wasan Manchester City Sau da kafa kuma suna fatan City din ta yi rashin nasara dan makinta ya ragu,yace yanzu lashe frieimiyane yasa a gaba.

Wasanni hudu da Salah ke magana shine wanda zasu buga da kungiyoyin Cardiff City, NewCastle United, Huddersfield Town da Wolves 

No comments:

Post a Comment