Sunday, 7 April 2019

Ina da kwarewar da zan iya zama shugaban kasa>>Babachir Lawal


Korarren sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal ya bayyana cewa, yana da cancantar zama shugaban kasar Najeriya, Babachir ya bayyana hakane yayin da yake inkarin yin amfani da tsarin karba-karba a zaben shekarar 2023 in Allah ya kaimu.

Da yake hira da jaridar The Sun, Babachir David Lawal yace, kowane bangaren Najeriya zai iya samar da shugaban kasar da ya cancanta.

Kasancewata mutum me hulda da mutane daga yanki daban-daban nasan mutane da yawa daga yankunan Inyamurai, Yarbawa, Hausawa, Ijaw kai harma da Kilba da zasu iya zama shugaban kasarnan kuma su yi abinda ya kamata, injishi.

Yace, kai ni kaina ina kallon kaina a matsayin wanda ke da kwarewar da zai zama shugaban kasarnan wanda ya fito daga kabilar da yawanta bai wuce 300,00 ba. Kuma akwai irin wadannan, kananan kabilun da yawa da zasu iya samar da shugaban kasa a kasarnan.

Ya kara da cewa kundin tsarin mulkin kasarnan bai haramta yin hakan ba.

No comments:

Post a Comment