Sunday, 14 April 2019

Ina jima Najeriya tsoron abinda zai faru a 2023>>Sarkin Musulmi

Sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar na III ya bayyana cewa yana jiwa Najeriya tsoron abinda zai faruba a zaben 2023 lura da yanda aka gudanar da zaben shekarar 2019, yanzu kan 'yan Najeriyar a rabe yake.



Sarkin ya bayyana hakane a wajan taron da kwamitin Dawa'awa ya gudanar a karshen mako a fadarshi dake Sakkwato. Ya kara da cewa a zaben 2019, malaman addini da ya kamata ace babu ruwansu da goyon bayan kowane dan siyasa amma sun fito kiri-kiri suna nunawa 'yan siyasa goyon baya.

Yace idan a 2019 an samu irin wadannan matsalolin to ina jin tsoron abinda zai iya faruwa a zaben 2023. 'Yan uwa basa magana da juna, haka abokai da makwabta saboda kamin zabe sun yi ta zagin juna.

Ya kara da cewa mu da muka shuwagabannin addini ya kamata mu yi hankali da abinda muke gayawa mabiyanmu saboda mafi yawanci basu da wadataccen ilimi dan haka duk abinda muka gaya musu zasu dauka gaskiyane. Ya kara da cewa yayi aikin sa ido akan zabe amma be taba nuna goyon bayan ga wani dan takara ba sannan bai taba gayawa wani malamin addini ya goyi bayan ko karya goyi bayan wani dan takara ba.

No comments:

Post a Comment