Monday, 29 April 2019

INEC na canja bayanan dake ma'adanar bayananta na sirri dan hana Atiku yin nasara a Kotu>>PDP

Jam'iyyar PDP ta zargi cewa, Hukumar zabe ta kasa me zaman kanta, INEC da mukarraban shugaban kasa, Muhammadu Buhari da canje-canje a ma'adanar bayanai ta hukumar zaben dan ganin cewa sun daidaita sakamakon zaben da suka bayyana cewa Buharine yayi nasara.PDP tace INEC din ta dukufa da wannan aikine saboda ganin cewa PDP din ta samu ainahin sakamakon zaben shugaban kasar kamar yanda yake a ma'adanar bayanan ta da kuma suka nuna cewa Atiku Abubakar ne yaci zabe.
 
Dan haka INEC din ke bi tana canja bayanan dake ma'adanar bayanan nata da kuma yiwa wadanda ma basu yi zabe ba makin cewa sun yi a rajistar zabe dan dai kawai su daidaita sakamakon da suka bayyana cewa Buharine ya lashe zabe da wanda ke cikin ma'adanar labaransu.

Saidai PDP di tacw abinda INEC bata sani ba shine ita kwamfuta da manhajojin dake cikinta na barin sahun duk wani amfanin da aka yi da ita.

No comments:

Post a Comment