Tuesday, 16 April 2019

Jami'an 'Yan Sanda Sun Kama Kananan Yaran 'Yan Shi'a 43 A Kaduna

Wasu gungun 'kananan yara Daliban Makaranta 'ya'yan Shi'a wadanda ake kira da ''yan Intizar' sun shiga hannun jami'an 'yan sanda jiya Litinin a garin Kaduna yayin da suka fito domin gudanar da wani biki.


Rahotanni sun nuna cewa an kama yaran ne a daidai 'Constitution Road' dake Kabala West garin  Kaduna, inda suka tsare su daga bisani suka kai su CID.

Bincike ya nuna cewa ba sau daya ba jami'an 'yan sanda a jihar ta Kaduna sun sha kama Mabiya Shi'an a duk lokacin da suka fito zanga-zangar lumana da wasu taruka tun bayan abinda ya faru tsakanin su da rundunar sojojin Nijeriya a watan Disambar 2015 suna kai su kotu, ko a kwanakin bayan nan wata babban kotu a jihar ta yi watsi da wata karar da Gwamnatin jihar ta shigar da mabiya Shi'an.
Rariya.


No comments:

Post a Comment