Tuesday, 16 April 2019

Jami'ar kasar Rasha ta yabawa wata 'yar Najeriya saboda gaskiyar data nuna

Wata jami'a a kasar Rasha me suna Michurinsk State Agrarian University ta yabawa wata daliba 'yar najeriya me suna, Asomba Nkiru Sandra saboda gaskiyar data nuna.A yayin da ake samun 'yan Najeriya da laifukan da basu dace ba a kasashen waje, ita Asomba Nkiru Sandra kuwa ganin kudi tayi a wajan na'urar cire kudi watau ATM kuma ba ta yi wata-wata sai ta kaiwa bankin rahoto aka bincika me kudin aka bashi abinshi.

Wannan abu da Asomba Nkiru Sandra ta yi yasa jami'ar ta shiga shafinta na yanar gizo ta yaba mata

No comments:

Post a Comment