Monday, 8 April 2019

Jariran bana ba zasu yi tsawon rai


Jinjiran bana ba zasu yi tsawon rai
Sakamakon wanibincike da aka gudanar a baya-bayan nan ya nuna cewa,jinjiran da za a haifa a nan  gaba a illahirin sassan duniya ba zasu yi tsawon rai ba.


An sanarwar da cewa hakan na faruwa sakamakon gurbacewar iska.Abinda yasa kowane jaririn da aka haifa a nan gaba rayuwarsa zai ragu da watanni ashirin (20).

 A cewar wani rahoton Babbar Hukumar Hasashen Yanayi ta Duniya (SOGA),gurbatacciyar iska na haddasa miyagun cututtuka wadanda suka danganci toshewar huhu,wadanda ke haddasa  mace-macen kashi 41 cikin dari na mutane,kashi 20 cikin dari na mutuwa da cutar siga,kashi 19 cikin dari na mutuwa da cutar kansar huhu, kashi 16 cikin dari na mutuwa ne sabili da cututtukan da suka jibanci zuciya.Kazalika kashi 11 cikin dari na mutane na mutuwa ne cutar bugun jini.

An tabbatar da cewa, wannan mummunan lamarin wanda ya samo asali daga gurbacewar iska zai fi cutar da nahiyar kudancin Asiya fiye da sauran kasashen duniya.

An sanar da cewa,tsawon rai yaran Kudancin Asiya zai ragu da watannin talatin,na yaran nahiyar bakar fata,wato Afirka zai ragu da watanni 24,a gabashin Asiya tsawon ran yara zai ragu da watanni 23,a Arewacin Afirka,tsawon ran yara zai ragu da watanni 18 da karshe a yankin Latin Amurka, rayuwar yara ta za rafu da watanni 9.

A jimillance, duk yaron da za a haifa a nan gaba a duniya,rayuwar za ta ragu da watanni 20.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment