Tuesday, 30 April 2019

Jaruman fina-finan Hausa 2 sun wa abokiyar aikin su duka bisa zargin satar dubu 60


Jaruman fina-finan Hausa biyu, Teema Makamashi da abokiyar aikinta, Sa'adiya Haruna sun zargi wata abokiyar aikinsu, Naja Ta Annabi da musu satar Naira dubu 60 inda suka dauki hoton bidiyon yanda lamarin ya faru suka watsa.

Shafin Kannywoodexclusive ya ruwaito cewa jaruman biyu sun daki Naja bisa wannan zargi. Sannan a wani faifan bidiyo na daban, bayan da bidiyon farko ya jawo cece-kuce, jaruman biyu sun bayyana cewa idan Najar 'yar uwar mutumce yai abinda zai yi.


No comments:

Post a Comment