Saturday, 20 April 2019

Jihohin da suka amince zasu biya sabon karin Albashin dubu 30

Bayan sakawa dokar karin albashi zuwa dubu 30 hannu da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi a makon daya gabata, wasu jihohin kasarnan sun fito sun bayyana matsayinsu akan wannan lamari.Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa gwamnatinshi ta dauki harkar kula da ma'aikatan jihar da muhimmanci shi yasa ma basa binta bashin albashi kuma a shirye yake ya biya sabon karin albashin da shugaban kasa yayi zuwa dubu 30.

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello shima ya bayyana amincewarshi da karin albashin duk da dai cewa ma'aikatan jiharshi na korafi da rashin biyan albashi amma yace a shirye yake shima ya biya sabon karin albashin da shugaba Buhari yayi, kuma yana fatan gwamnatin tarayya zata saukaka hakan.

Gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari shima yasha alwashin fara biyan ma'aikatan jiharshi sabon karin albashin.

Hakanan gwamnan jihar Osun, Mr. Gboyega Oyetola shima yace zai jira takardar umarnin yanda za'a fara biyan sabon karin albashin, yace da zarar takardar ta shigo hannunsu to zasu yi dukkan abinda ya kamata.

Gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed shima yace gwamnatinshi a shirye take ta biya sabon karin albashin dan inganta rayuwar ma'aikatan jihar.

Hakanan itama gwamnatin jihar Naija ta amince da biyan ma'aikatanta sabon karin albashin.

Gwamnatocin jihohin Delta, Rivers, Cross-River, da Edo duk sun amince da biyan sabon karin albashin na dubu 30, kamar yanda The Nation ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment