Tuesday, 16 April 2019

Ka fito da takardar WAEC dinka idan da gaske kana da ita>>PDP ta gayawa Buhari

Jam'iyyar adawa ta PDP ta kalubalanci shugaban kasa,Muhammadu Buhari da ya fito da takardarshi ta kammala makarantar Sakandire idan yana da ita. PDP ta yi wannan maganane bayan da me magana da yawun kwamitin yakin neman zaben Buharin, Festus Keyamo yace ba sai mutun na da takardar ta sakandire ba zai iya tsayawa takarar shugaban kasa.A sanarwar data fitar ta hannun me magana da yawun ta, Kola Ologbondiyan PDP tace, waccan magana ta Festus Keyamo ta nuna cewa shugaban kasar be da takardar kammala sakandire kenan kamar yanda ya fadawa INEC cewa yana da ita .

PDP tace a matsayinshi na me gaskiya be kamata ya fadi cewa yana da abinda bashi dashi ba dan haka idan yana dashi ya fito ya nuna bawai a dauke hankulan mutane ba ta hanyar turo me magan da yawunshi yana fadar wasu abubuwan da ba na kamawa ba

No comments:

Post a Comment