Friday, 26 April 2019

Kalli yanda wani murgujejen maciji dake tsallaka titi ya hana masu motoci wucewa

Wadannan hotunan wani katoton macijine da aka gani akan titi a hanyar wani gari dake kasar Brazil. Wani matafiyine ya fara ganin macijin inda ya tsayar da motarshi dan baiwa macijin damar wucewa.



Mutumin ya bayyana cewa, yana cikin tafiya sai yaga macijin sai ya tsayar da motarshi dan baiwa macijin damar wucewa, ya kara da cewa ya sha ganin matattun macijai da motoci suka kashe akan hanya wanda kuma abin baya mai dadi shiyasa yace bari ya baiwa wannan macijin dama.

Bayan tsayawar mutumin, wasu sauran direbobi da dama sun bi sahunshi inda suka tsaya sannan akaita daukar macijin hoto a yayin da yake tsallaka titin.

Mutane da dama da suka shaida wannan lamari sun ta saka hotunan yanda abin ya faru a shafin Facebook.





No comments:

Post a Comment