Saturday, 20 April 2019

Karanta hirar Wani sarki a jihar Zamfara da shugaban 'yan bindigar jihar data bayyana

Wata hira da wani sarki a jihar Zamfara yayi da daya daga cikin shuwagabannin 'yan bindigar jihar ta bayyana inda aka ji suna tattaunawa akan cewa kawo jami'an tsaro jihar zai kara yawan zubar da jinine maimakon kawo karshen shi.Jaridar Punch ta ce ta samu kwafin muryar da aka nada ta hirar sarkin da ba'a bayyana sunanshi ba amma ana tunanin yana yankin Zurmi ne na jihar ta Zamfara, anji sarkin da wani shugaban 'yan bindigar na hira, Punch tace ta samu kwafin muryarne daga wata majiya daga hedikwatar soji.

A cikin muryar an ji shugaban 'yan bindigar na cewa an kawo sojoji da 'yan sanda sun kashe mai 'yan uwa mata da 'ya'ya, irin haka zubar jinine kawai zai kara sawa, yace yana bukatar sarkin ya rushe kungiyar 'yan sa kai na kato da gora sannan ya zauna da manyan mutane a yankin a samu hanyar maslaha amma ba wai ta hanyar soji da 'yansanda ba.

Yace harin da sojojin ke kawowa ta sama baya samunsu domin duk sanda jirgi zai kawo hari, kamin ya taso sun samu bayanin inda zai kai hari, dan haka suna barin gurin saidai su kashe tsintsaye.

Ya kara da cewa, ko da sojojin kasa da ake aikowa kamin su zo sun san da zuwansu, dan haka suke shirya musu.

An ji sarkin na amsawa shugaban 'yan bindigar da hakane a maganganun da yake da kuma cewa suma basu goyi bayan kawo jami'an tsaro jihar ba sannan a akarshe ya amsa cewa zai rusa 'yan kato da gora a yankin sannan zai zauna da manyan yankin da samo hanyar maslaha.

Hukumar tsaro dai ta zargi cewa akwai hannun wasu sarakuna a hare-haren na jihar Zamfara abinda sarakunan suka karyata.

No comments:

Post a Comment