Saturday, 6 April 2019

Karanta martanin Adam A. Zango akan cece-kucen da ake yi kan ikirarin da yayi na cewa ya fi kowane Bahaushe sun a Duniya


Bayan cewa da yayi ya fi kowane Bahaushe suna a Duniya kuma lamarin ya dauki hankula sosai, Adam A. Zango ya mayar da martani akan cece-kucen da ake yi akan ikirarin nashi.

Adamu ya saka wadannan hotunan na mashahuran mutanen Arewa inda yace shi ya godewa Allah da har ake hadashi da manyan mutane irin wadannan kuma ai ba yin kanshi bane yin Allahne, wanda kuma yake ganin zai iya hana ruwa gudu to sai ya gwada.

Adamu yace ga masu shakku akan ikirarin nashi sai su je su yi bincike.

Ya kuma ce kada a rudeku da yawan mabiya a shafukan sada zumunta saboda shi ba tun yau ya fara ba, tun kamin zuwan Facebook, da Intagram aka sanshi.

Ga dai abinda ya rubuta kamar haka:

No comments:

Post a Comment