Saturday, 13 April 2019

Karanta martanin Atiku ga APC akan cewa da suka yi shi badan Najeriya bane

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ya mayarwa da jam'iyyar APC da martani akan cewa da ta yi shi ba dan Najeriya bane dan kasar Kamarune dan haka be ma kamata a barshi ya tsaya takarar shugaban kasa ba.Da yake mayar da martani ta hannun me bashi shawara akan kafafen watsa labarai, Paul Ibe,Atiku yace bazai mayarwa da APC martani ba, Lauyoyinshi zasu dauki matakin daya kamata a kotu.

Saidai ya jawo hankalin kotun da cewa yana fatan ba zata bayar da dama ga wannan ikirarin na APC ba, ta daukeshi a matsayin shirme,Atiku ya bayyana cewa ya yi aiki a kasarnan sannan ya shiga siyasa inda ya zama mataimakin shugaban kasa kuma ya samar da ayyukan yi na kaitsaye da wanda bana kai tsaye ba

No comments:

Post a Comment