Sunday, 7 April 2019

Kisa da satar mutane dake faruwa a Zamfara na matukar damuna>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buharu ya bayyana damuwarshi akan kisan da 'yan bindiga ke yi da kuma satar mutane dan kudin fansa a jihar Zamfara.Hadimin shugaban kasar, Bashir Ahmad ne ya bayyana haka ta shafinshi na Twitter inda yace, da shugaba Buhari ke mayar da martani akan kisa da satar mutane dan kudin fansa da ake yi a zamfara, ya bayyana cewa shima abin na damunshi.

Yace ta yaya za'ace ban damu da abinda ke faruwa ga mutane 'yan uwana ba? nima mutumne nasan irin zabin da wanda aka kashewa 'yan uwa da wanda aka sacewa 'yan uwa aka karbi kudin fansa suke ji, shugaban ya kuma mika sakon ta'aziyya ga wadanda suka rasa 'yan uwansu a jihar.


No comments:

Post a Comment