Tuesday, 9 April 2019

Kofi daya na giya na iya kawo shanyewar rabin jiki

Shan barasa kadan ko daidai gwargwado na kara barazanar kamuwa da hawan jini ko kuma yiwuwar samun cutar shanyewar rabin jiki kamar yadda wani binicike ya bayyana.


Wannan binciken dai ya kalubalanci wani bincike da aka gudanar a baya da ya bayyana cewa shan giya sau daya ko sau biyu a rana ba wata matsala bace.

Binciken mujallar 'The Lancet' mai fitar da labarai kan sha'anin lafiya ta gudanar da wannan binciken.


Masu bincike a Ingila da China sun yi nazari kan 'yan kasar China kusan 500,000 a shekara 10.

Masana sun bayyana cewa yakamata mutane su rage yawan barasar da suke sha.

Tuni aka san cewar shan barasa fiye da kima babbar barazana ce ga lafiyar bil adama da kuma yiwuwar samun cutar shanyewar rabin jiki amma duk da haka wasu binciken sun nuna cewa shan barasar kadan na kara lafiya, wasu kuma suka ce babu wani mizanin shan barasa da za a ce mutum ya tsira.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment