Sunday, 28 April 2019

Ku kwantar da hankalinku masoyana, Zan zama shugaban kasa, sai na kwato zabena>>Atiku

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya baiwa magoya bayanshi tabbacin yin nasara a kotu inda yace mutane miliyan 18 da suka zabeshi su kwantar da hankalinsu zai kwato zaben shi da yaci.Atiku yace a tarihin kotun sauraren karar zaben Najeriya ba'a taba samun wanda ke da shedu karara kamar nashi ba dan haka su kwantar da hankalinsu shine zai yi nasara.

Atikun ya bayyana hakane a wata sanarwa daya fitar ta hannun me taimakamai kan lamuran matasa, Ambasada Aliyu Bin Abbas kamar yanda Daily Post ta ruwaito.

Atiku yace yasan mutane da dama sunsha wahala kala-kala wajan zuwa kada kuri'unsu, wasu sun yi tafiya me nisa, wasu ma basu taba zabe ba sai a wannan karin, wasu har kudi suka rika biya dan a basu katin zabensu dandai su ga sun samu Najeriyar da tafi tada amma sai gashi tsoron shugaban hukumar zabe, INEC ya kawo musu cikas inda ya baiwa APC nasara.

Yace duk a kwantar da hankali, kotu inda nanne kadai talaka ke da karfi, yana fatan zasu yi adalci ba tare da tsoro ko nuna fifiko ba wajan yanke hukunci.

No comments:

Post a Comment